Assalatu wassalamu alaika
kar'she da farkon matsayi,
jigo asalin isa da dukkan matsayi,
kai ne gatan isa da duk nau'in matsayi,
kai ake bi in ana buka'tar matsayi,
jeka ka gaida shugaba kai matsayi,
Almustapha, shugaban duk matsayi,
yardar sa ce tasa ka zamto matsayi,
in ba dan kaiba Almustapha
da ba bu kalmar matsayi,
kai barima na rantse da ubangijin ka
kai ne matsayi,
farko, tsakiya da kar'shen matsayi,
masoyin ka da kansa yake yabon ka
dan matsayi,
ya yi kiran ka har zuwa fadar sa
ko'loluwar matsayi,
ahalittun sa kai kadai' ka taka
harga wannan matsayi,
ya yi maka sallama ya shugaba mai matsayi,
ku ka tattauna ya baka sakon' matsayi,
sai ranar da ake takai-takai
za a sanka gun matsayi,
a ranar da masoyin ka
za ya baka tutar matsayi,
na rantse da buwayar sa ubangijin ka
shi ya sanka gun matsayi,
duk girman kalma ta koma ka'rama
gurin yabon mai matsayi,
ina rokon' tabara sarkin matsayi,
ya yi min arzikin' saninka ya mai matsayi,
tarin basira ya dutsen uhudu
gurin yabon mai matsayi.
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem