Dokin Kar'fe 1 Poem by Garba Ado Ibrahim

Dokin Kar'fe 1

Dokin karfe kadai'
ake hawa a zauna lafiya.
Ba wani shan wuya ko zancen magiya,
akai ruwa rana ana ta du'ra ashariya.
Gwanin sukuwa ba din'gishi,
targade' ko yin karaya,
a kafar ki ko a cikin zuciya.

Rungumar ki kawai ya ishi bawa kariya.
Ba girman kai akan dau'kar ki a kariya.
Cutar da ke kashe bawa a mummuke',
ku'lle cikin zuciya.

Dokin karfe ruwan ki na sha ya fi mada'ciya.
Ciyawar ki ke tumurmusa darbejiya.
Ma su kaunar dokin kara,
na ganinki a tumfafiya.
Ba rabon su makaho a wasan bakin rijiya.
Kul! Kar ka hau da rana kuka ko tsamiya.
A hawan ki ba su rago ma su yar' ka'ramar zuciya,
bare su wane da wane ma su yar' yayen zuciya.
Hannu da yawa maganin su ka'zamar miya.

Sukuwa akan ki dadi' in an iya,
musamman gun mai juriya.
Uhm! Hawan ki ba su Talatu da Ladidiya,
su a su wa kare da gudun laiya.

La! Ga su Laure da Sadiyya.
Mahayin ki ka'far sa a duniya.
dayar gidan ta a gefen duniya.
mahayin ki na da kansaka'li,
bindiga da mashi har kibbiya.
Abokin ki ya kan zamo kamar
cikin tsuntsaye mujiya...

Tuesday, November 13, 2018
Topic(s) of this poem: nature
COMMENTS OF THE POEM
READ THIS POEM IN OTHER LANGUAGES
Close
Error Success