Da farko ina sanar daku aniyar takara,
Ita ce hujjar da ke ingizani,
In tona muku kogin fura,
Koda da aniyata in jawo muku fanfon fura,
Saboda rawar da take tika',
Can acikin bazzara,
Da ko'ka'rinta gun ma'abota furfura,
Amma ku sani ni da ku amana ce ko ba takara,
Ina masu rubutu a rubuta zan kogin fura?
Asamu gonaki manya sha tara,
Ahade' guri guda maza ayi hattara,
Ni cikin tafiya ta ba yaudara,
Halin kaka na na goma can bakin Jakara,
Kun sanni dan' cikin ku ne
Ba bu batun hijjira,
Duniya da yalwa in an matsa,
Matsa ba zancen takura,
Tunanin ku da kau'nar ku,
Ke saka ni a halin tara,
Na sha kukan tausayin ku wane mako tara,
Ku dai ku cicciba' ni in samu in ke'tara,
Nan za ku gane na san ki'mar birni har karkara,
Asalin mai usuli nanne tushen kara,
Hakane mai girma mai kogin fura,
Inji zagin mai kogin fura,
Da ma ku saurari batunnan a cikin hattara,
Yallabai' mai kogin fura?
Ba wargi ko a zauna ayi hira,
A a yaro inji wani dattijo cikin furfura,
Kar abarmu washe akan marmara,
Ko sai wani jikon' karon kare.
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem
kar abarmu washe akan marmara, nice,10