Al'amarinki na da aminci
mai ban tsoro.
Duk girmanki ba ki,
da kimar fiffiken dan' sauro.
Rashin sani gudun bazawara,
da karen gwauro,
da ango sabon sunan gwauro.
Kina kai mutum kuryar daki,
ko ki adana shi a soro.
Farin wata fitilar duniya,
adon sama sai tauraro.
Ko kin san akan batu bana kwauro?
Na dau darasussukan ki,
har iyau ina sauraro.
Kina da tsauri tamkar marmaro
Kina nuna son ranki,
cikin duk taro.
Wanda kuke kallon-kallo,
ki barshi ana mai karo-karo.
Kina da karancin tausayi,
irin na mugun kwa'ro.
Kin iya kwalliya gaki da doro.
Wanda ya soyu dake,
ki kai shi inda za ki baro.
Mai gudun ki,
shi ki ke so ki taro.
Tabbas, al'amarin ki na da ban tsoro,
amma ga wanda ke da baiwar tsoro,
ba ga wanda kan tsaya
gaban ki ba sororo,
ko kuwa masu fadin Allah koro-koro.
Ni dai kina firgita ni,
gashi ki ban tsoro,
amma ina rokon buwayi baiwa ta tsaro,
ya tsare ni kar ki kaini karshen soro,
ki sa adinga nuna ni ataro,
dan karfin ki na kama da,
na giwa mai mukamin toro.
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem