Ke rayuwa ki fada'mana wai ina za ki damu, kin kwashe mu lungu kwararo kina ta kwarabniya damu, al'amarin ki na da ban tsoro hakama inji Adamu, mai hankali ke gane ki akasin haka an gamu, in mishkilancin ki ya motsa ki tuna ki manta damu, na kiyaya kan sabgar ki dan hakan shi yasa ni na damu, na kasa zaune na kasa tsaye kin sa na kidi'mu, ki kan ja mutum a jiki har sai kin ga ya kamu; ko ya fara fankama ya na ganin ya samu, ba ki da tabbas asa'ilin za ki sa ya tumu, sha'anin ki sai haku'ri mai ka'rancin sa zai damu, bi rayuwa a sannu kar ki dinga ke bamu, mazan jiya maganin mazan yau a fagen yin gumu, in Allah ubangiji ya so mu, ke duniya ki' mu, yau da gobe duk daya ne agun sa Allan mu, lalba' rayuwa ko dan gudun agamu, ko aje ba shiri a tumu, mu yi haku'ri duk tsawon dare a yi damu, kar mu dinga gaggawa muna gamu-gamu, gujewa aikin sheda'n in ka ki' za ku gamu, kar'she yama gwalo acan lahira ka tumu.
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem