Taki Poem by Garba Ado Ibrahim

Taki

Taki sannu da fama barkan ka da ko'ka'ri, gatan gona zuba ka ka sa amfani aga yayi kauri, duk girman gona in ba bu kai ta fi kwari, rashin ka kan sa gari afari, kaga rusheshen ka'to jikin sa nata ba'ri, saboda yunwa ja'ira bata jin abari, gatan manoma ko su fada' tudu da kwari, idanda tudun ne da sun huta da kwari, azuba ka kadan' amfanin gona ya ku're, kin zuba ka yaja amfanin ya ba're, in an gumbuda' ka sai yabanya ta ware, kaga an dafo tuwo ana yawon rabo atire, aikai taki in ba bu kai ba bu noma, in ba bu noma ba manoma, in ba manoma ba makama, in ba makama ba manema, in ba manema ina matsayin makoma? Ashe taki kai ne gatan gona har masu noma? Gurin neman ka manoma nata fama, ya manomi zai ji aneman ka dan tserewa kyarma? yasha farar wahala fat ba makama, yasaduda yadawo gona ba makoma, yana shiga gona yagan ka kana barci atabarma, kar'ka'shin inuwar dawa ga munshari na alfarma, dan tsananin tsabar murna zai so ya suma, dan ko ba komai zai tserewa gulma, sannan ga ka akyauta har manema.

Saturday, December 1, 2018
Topic(s) of this poem: nature
COMMENTS OF THE POEM
READ THIS POEM IN OTHER LANGUAGES
Close
Error Success