Ya shugaba barka da sauka ma'aiki ba ka da tamka, farko da sunan ubangijin ka, shugaban duk masu son ka, Allah gwani mai rani da ka ka, salatin ka ba iyaka, ga jarimin da bai da tamka, manzon da kyawun sa ba iyaka, Allah ne yake yabon ka, matsayi da muka'mai duk ya ba ka, maki'yan ka ke asara mala'iku su sa mu su tafka, kalma na da rauni agun yabon ka, ya shugaba ba mai kyautar ka, khairul anam in kyautar sa ya ba ka, ka rada' mata sunan marka-marka, ai yabo sai wanda ya sanka, shine ubangijin ka, shi ya sanka ya san matsayin ka, ya mai birnin madina da birnin makka, saboda cikar matsayin ka, mala'iku suna yabon ka, ya abul Alkasim sheda'nu ma suna yabon ka, ina gamu mabiya agare ka? Ya shugaba na mutum aljan da mala'ika, masoyi daya tal jal tak, wanda ba ka da tamka, ya wanda Allah ke wa kirarin da ba iyaka, ka yi min kyautar aljanna dan isar ka, dan daraja da alfarmar da rabbana yabba ka, ya masoyi na almalik, dan Fadi'matu, ya' tsoka da jinin ka, dan Hasan da Husain jikoki agurin ka.
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem