Gadon Bacci Poem by Garba Ado Ibrahim

Gadon Bacci

Gadon bacci kar'shen,
Su inna kwarabniya,
Akai mari akai gwauro,
Kan ka ake kwanciya,
In an gyara ka gun bacci ayi dariya,
Wofantakka ke tono tsiya,
Kulawa daya,
Bayan wani zamani ta koma miliyan daya,
Murmushi kana ramashi da dariya,
Mai nuna ka da yatsa sai masoyi,
Agurin tsiya,
Ko mai kau'nar shiga cikin,
Daular yan'tsiya,

Kai akewa hidima agama lafiya,
Kamar ka na da kamalar bulaliya,
Hanji ka ke tamkar bashi,
Mai ci sai ya biya,
Kyawun ka na da nagartar zinariya,
Kana da sheki' tamkar zara ta taurariya,
Kana da albarka tamkar maliya,
Ba ka raina kulawa,
Ko ka'rama sai ka biya,
Duk tsawon zamani,
Cikin mutunci ga godiya,
Ko ankai da shekaru zambar miliyan daya,

Yinka na da dadi' sai ku'nar zuciya,
Gyaran ka na buka'tar yin haku'ri,
Gami da juriya,
in an kimtsa ka nishadi',
Ga hasken zuciya,
Gadon bacci sannu danko' sarkin godiya,
Ba ka fadu'wa ka'sa banza sai kai gayya,
Gadar arzikin' ka sai mai zuciya,
Ni na sheda yinka na da ribar zinariya.

Saturday, November 17, 2018
Topic(s) of this poem: nature
COMMENTS OF THE POEM
READ THIS POEM IN OTHER LANGUAGES
Close
Error Success