1. Na rasa me ma za na ce
Kyan sama ya yi talau-talau!
2. Hairi gare ni yana tafe
Gona ta kwananta ƙalau
3. Babu haki ba hancin kare
Yabanya ta yi falau-falau
4. Na bata taki kalar ƙwarai
Yai mata daɗi kamar marau
5. Mai nema dai yana sane
Jallah kaɗai ke ba shi lau
6. Burin mai ilmi ya kai
Ƙolin ilmi can ya hau
7. Duk sanɗa duk rarrabe
Mai niyya kan ishe ƙalau
8. Haske da duhu ba su ɗai
Mai kitsa sharri ja shi talau
9. Me ma ai zai ɓatanka rai?
Haƙuri ɗauki farau-farau!
10. Mai haƙuri shi ne tafe
Ɗacin haƙuri ya yi ƙarau
#Hausa #Dr.Ibrahimlawalsoro #Soyayya #Sama #Falcao
© Dr. Ibrahim Lawal Soro
07.09.2022 CE
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem