Mai Haku'ri Poem by Garba Ado Ibrahim

Mai Haku'ri

Mai haku'ri shi ka shan sa,
Romon dutse,
Mai sara bi sannu,
Dan gudun yin sartse,
Gulmamme an shaida,
Ka na da baiwar kutse,
Zaki mai arhar kar'fi,
Da nufo gari a watse,
Sadauki na da shahada,
Irin ta baiwar dantse,

Kai haku'ri!
Na san halin ka,
Yin ka sai an rintse,
Sai mai zuciya ya kwa'rin dutse,
Mai dace da ya gama,
Fushi za ya katse,
Fatana sako'na,
Yaje ga birnin Dutse,

Kul yaro!
Banda wasan dutse,
Acikin sa akwai arzikin' yin rotse,
Gardamamman jaki ka sa aranka,
Sai ya tustse,

Mai haku'ri tafiyar ka,
Tafi kar'fin sartse,
Hankalin ka na da mugun kyawun da,
Duk dafi kan tatse,
Juriyar ka kansa har cikin wuta,
A dau'ko shi kitse,
Duk tsaba ko tsanani gare ta,
Tsatsa za ka katse,
Masoyi ka ke gun Allah,
Zuciyar ka daure ka matse,
Ana yi maka kallon rogo,
Kai ka na yin na kitse,

Du ka ba ku ka,
Farin cikin ka duk an gimtse,
Sannu damo,
Bakin' cikin ka duk ka guntse,
An dade' ana tafka ruwa,
Ayau ka'sa ta tsotse,
Rayuwar su kacokan,
Duk alheri gare ka sai sun totse,
Ba zama ba tsayuwa,
duk sun motse.

Sunday, November 18, 2018
Topic(s) of this poem: nature
COMMENTS OF THE POEM
READ THIS POEM IN OTHER LANGUAGES
Close
Error Success