Sunan ka ne a farko, ya mai kar'fin da sai dai ace mamako, kar'fin sa ne yake sa mai dogaro ya tsallake duk tarko, da safe kamun fara sai mai sammako, ya buwayi sarki mai iko, mai halitta iri daban-daban a cikin su da fifiko, fari baki' da dogo dan'kasuwa, manoma yan'boko, sammai da ka'san bakwai, kwanakin su ka'san mako, mutum mala'ika da aljan, wata dabbar tana da tako-tako, ba ka da kar'she buwayi ba maganar farko, aljanna gidan hutu daki-dakin wuta ko gidan narko, mai rahama, adalci da karamcin da shugaba ke koyo, ya mahalicci, tsayayye bisa bayi, mai haku'ri da taimakonda ya wuce tsinkayi, tsarki da kadai'ta gareka ya mabuwayi, masoyi ga shugaba majingina agurin bayi, salatin da tunanin mutum ba zai gane ba, ga annabi shugaba, mai muka'mi babba, ya mawadaci mai mulkin da tunani ba zai gane ba, mai godiya da kyauta irin ta girma babba, kai tunani, bace min da gani ba ka gane sarki rabba, sanin ubangijin mu ba dai kai ba, sai dai shugabanyan' aike da annabawa babba, kar'fi da buwaya gareka sarki rabba.
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem