Wakoki Na 1 Poem by Garba Ado Ibrahim

Wakoki Na 1

Ko ba dade ko bajima duk mai rai sai ya bar duniya, wannan alkawarin mamallaki ne mai duniya, wani zai barta ne yana tsakar jin dadin miya, wanda ya dace ko yana cikin sharbar wu ya, mutuwa riga ce a sakale can a bisan wuya, in na bar duniya, kar ku kyale masu ci min dunduniya, kun ji wakoki na? Ku tabbata su ma sun sha wu ya, ku kai mari ku kai gwauro ku sa su cikin tsiya, wakoki na Allah ya yi muku albarka jariya, ya baku kafafu irin na barewa ta sha kunyar ta tsiya, ta yi kwanan bakin ciki da kakarin wu ya, ta dinga marisa tamkar wata yar' giya, in ana magana ku yi sauraro ba dariya, ita dariya tana kama da siffar yan' fariya, ko izgili da girman kai ba ki daya, takama da jin kai ne kai daya, siffar ilahu mai wahadaniya, in na bar duniya, wakokina za su tattara kaya, cikin kewata su fara yin yawon duniya, su bar makiya cikin takaici da kwarabniya, asa'ilin za su azurta da ciwon zuciya, kiki-kaka sai ka ji su abayan duniya, mai Allah a rai ya taushe dirkaniya, dare-dare bisan ta ya yi gwalo ga dariya...

Sunday, November 11, 2018
Topic(s) of this poem: nature
COMMENTS OF THE POEM
READ THIS POEM IN OTHER LANGUAGES
Close
Error Success